Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A cikin Sanarwa Na 22 ta ayyukan Wa’adis Sadiq 4 da cibiyar yada labarai ta IRGC ta fitar: a safiyar yau Juma’a sun aika gungun makamai masu linzami nau’ikan Khorramshahr 4 da Khaibar da Fattah da razmin “ Husain bin Ali “ a kokarinsu na daukar fansar ga kisan gillar da aka yiwa yaran Iran a makarantar Minab, inda ta harba su akan wuraren Amurka da gwamnatin sahyoniyawa da ke Tekun Farisa zuwa Tel Aviv.
A cikin wannan hari mai ƙarfi, hare-haren an yi su ne tare da makamai masu linzami masu ƙarfi, "Khorramshahr 4" babban makami mai ƙarfi da ke dauke kawuna da babban sauri "14 Mach" an aike su zuwa ga wuraren mugayen abokan gaba na al'ummar Iran.
Sansanonin Amurka da ke Tekun Fasha da wuraren Isra’ila da wurare a Tel Aviv da Filin jirgin saman Ben Gurion da sansanonin soji na Haifa sun fuskanci makamai masu linzami na New Generation.
Cikakkiyar nasarar harba wadannan makamai masu linzami daga jerin sansanin makamai mai linzami na IRGC a rana ta bakwai na yakin ya karyata ikirarin raunanar dakarun tsaro da rage yawan makami mai linzami da harba UAV ta hanyar yada wannan farfaganda ta girman kai.
'Ya'yan sojojin Iran masu kishi na ci gaba da yakin cikin izza a yankin akan manufofin Amurka da gwamnatin masu cin zarafi. Shirin nasarar fagen fama tana hannun Jamhuriyar Musulunci
Ra'ayinka